Kotu Ta Bayar Da Belin Emefiele Bisa Wasu Sharuɗɗa



Babbar kotun tarayya a birnin Legas ta bayar da belin gwamnan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele a kan naira miliyan 20, bayan ya shafe mako shida a hannun hukumar ‘yan sandan sirri ta DSS.

Mista Emefiele ya ƙi amsa laifin da ake tuhumar sa a kai guda biyu na mallakar bindiga guda ɗaya da harsashi 23, zargin da rundunar ‘yan sandan sirri ta gabatar.

A ranar Talata ne gwamnan bankin da aka dakatar ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya bayan umarnin wata kotu na gurfanar da shi ko kuma a sake shi daga hannun hukumar DSS.

A watan jiya ne, hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sanar cewa Emefiele yana hannunta kwana guda bayan dakatarwar da shugaba Bola Tinubu ya yi masa daga aiki.

A hukuncin da aka yanke a ranar Talata, alkalin kotun ya bayar da umarnin a tsare Mista Emefiele a gidan yari na Ikoyi, da ke Legas har sai an kammala cika ka'idojin belinsa.

"An dage sauraron ƙarar zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba."


Rahoton BBC Hausa 

Post a Comment

Previous Post Next Post