DA ƊUMI-ƊUMI: Jami'ar Abuobakar Ibrahim dake Maradi Ta Ƙaryata Batun Cewa Young Sheikh Zaria Ya Kammala Digiri A Jami'ar.


Jami'ar Abuobakar Ibrahim da ke birnin Maradi, ƙasar Niger ta yi watsi da zancen da ke yawo a kafafen yaɗa labarai na cewa Young Sheikh Zaria ya kammala karatun digiri a jami'ar. 

Cikin wani saƙo da mataimakin shugaban jami'ar (DVC) Muohammad Abuobakar Lawwali ya fitar, yace Young Sheikh ɗalibi ne yanzu haka a jami'ar, kuma sun bashi gurbin karatu a shekarar 2021 bayan ya nema ta Internet da takardun NECO da IJMB da kuma takardan Declaration Of Age mai ɗauke da shekaru 15 zuwa 16.

Sannan sun bayyana cewa basu san yadda Young Sheikh ya samu rigar kammala jami'ar ba domin kuwa yanzu yana aji 1 ne zuwa biyu. 

Jami'ar sun buƙaci Young Sheikh da ya fito ya ƙaryata batun labarin da ake yaɗawa kan kammala karatun digirin sa a jami'ar idan ba haka ba, zasu iya ɗaukan matakin shari'a akan ɗalibin. 

Me zaku ce kan wannan tirka-tirka na Young Sheikh? 

Daga Abba Ibrahim  

Post a Comment

Previous Post Next Post