Ƙungiyar Al-hilal Ta Ƙasar Saudiyya Ta Taya Mbappe Kan Fan Miliyan 300


Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Hilal ta Saudiyya ta gabatar da tayi mafi gwaɓi a tarihi na fan miliyan 259 a kan ɗan wasan PSG, Kylian Mbappe, kamar yadda kafar Press Association ta ruwaito.

Ɗan wasan mai shekara 24, wanda ke da sauran kaka ɗaya a kwantaraginsa da PSG ya ƙi sanya hannu kan sabon kwantaragi, kuma ba ya cikin tawagar ƙungiyar da za ta buga wasannin sada zumunta gabanin fara kaka mai shigowa.

PSG na son ta sayar da Mbappe a yanzu a maimakon barin sa ya tafi a kyauta a baɗi.

Tafiyar ɗan wasa Neymar daga Barcelona zuwa PSG kan kuɗi fan miliyan 200 ita ce cinikin ɗan wasa mafi tsada a tarihi ya zuwa yanzu. 

BBC Hausa 

Post a Comment

Previous Post Next Post