Hukumar Yaƙi Da Cin-hanci Da Rashawa Ta Gayyaci Ganduje Domin Tambayoyi Kan Bidiyon Dala


Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, ta gayyaci tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje domin amsa tambayoyi kan faifan bidiyon dala da ya taso.

A ranar Laraba, shugaban PCACC, Muhuyi Magaji-Rimingado, ya bayyana cewa an tabbatar da sahihancin bidiyon.

Da ya ke jawabi a wani taron kwana daya da aka gudanar a kan ‘Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Kano’, Rimingado ya ce an gudanar da binciken ne a kan faifan bidiyon kuma ya nuna cewa na gaske ne.

Da ya ke fitar da sanarwa a yau Alhamis, kakakin hukumar yaki da cin hanci, Kabir Abba-Kabir, ya ce an gayyaci tsohon gwamnan ne domin amsa tambayoyi.

A cewar Kabir, Mista Rimingado, wanda ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a matsayin bako a shirin Siyasa na Channels TV a yau Alhamis, ya ce hukumar na sa ran tsohon gwamnan zai gurfana a gabanta mako mai zuwa domin ya wanke kansa a cikin binciken da ake yi.

Yayin da yake amsa tambaya kan ko hukumar za ta ci gaba da gudanar da binciken ko a’a, Mista Rimingado ya ce: “Na sanya hannu kan wata takarda na gayyatar shi domin yi masa tambayoyi a hukumar a mako mai zuwa domin wannan shi ne abin da doka ta ce, kuma za mu ba shi dama don ya kare kansa.”

Da aka kara tambayar sa kan abin da hukumar za ta yi idan gwamnan ya kasa bayyana, shugaban ya ce: “Akwai abin da doka ta tanada a kan haka." 

Post a Comment

Previous Post Next Post