YADDA AKA TSINCI WATA JARIRIYA SABUWAR HAIHUWA A WATA BABBAR ASIBITIN GWAMNATIN TARAYYA.




A ranar Alhamis ne rahotonni suka bayyana cewa an tsinci wata jaririya wanda ba'a san ko ɗiyar wacece ba a bayan wurin karɓar haihuwa na assibitin gwamnatin tarayya da ke Birnin Kebbi.

Wani shaidan gani da ido da ya buƙaci a sakaye sunansa ya tabbatar da cewa tuni ma'aikatan jinya da Ungozoma na 
asibitin suka ɗauke jaririyar .

Wata majiya ta sheda min cewa "Ita dai jaririyar nan an ganta ne a bayan wurin kula da masu haihuwa (maternity complex FMC Birnin Kebbi) wanda ya ganta ne ya kira jami'an tsaron asibitin, inda su kuma suka duba tare da isa ɗakin haihuwa (Labour room) sannan suka kira  jami'an da ke aiki a wurin. 

Bayanai sun nuna cewa koda aka ga jaririyar tana tare da uwar tafiyar ta (placenta).

Sai dai wani jami'in tsaro a asibitin da shima ya buƙaci a sakaye sunansa yace "suna ganin kamar ba'a nan ne aka haifi jaririyar ba, saboda  yanayin da take da ƙasar da ke tare da ita a jikin ta ya banbanta da wanda ke wurin, saboda haka suna ganin kamar an ɗauko tane daga wani wuri aka kawo aka aje ta a bayan wurin haihuwar na asibiti ta FMC Birnin Kebbi"


Bayanai dai sun nuna cewa jaririyar tana cikin ƙoshin lafiya, kuma tuni aka ɗauke ta zuwa ɗakin kula da jarirai (SBU) na asibitin, sannan an damƙata ga wata jami'ar da ke aiki a wurin  kuma tana ƙarƙashin kulawar su.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton majiyar ta tabbatar mana da cewa ba'a samu wani bayani akan wanda keda mallakin wannan jaririyar ba, ko wani  bayani akan ta ko kuma wanda ya kawo ta wurin.

Daga Dahiru Kasimu Adamu

Post a Comment

Previous Post Next Post