Labarin Cewa An Naɗa Ni Shugaban EFCC Ƙarya Ne - Odumosu

Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya mai ritaya, Hakeem Odumosu ya ƙaryata labarin naɗa shi a matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC.

Labarin nadin na Odumosu ya yi kamari yaɗu a jiya Talata a shafukan sada zumunta daban-daban ba tare da danganta shi ga wata kafa sahihiya ba.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba, shugaban ‘yan sandan mai ritaya ya ce bai san da irin wannan nadin ba.

Ya siffanta labarin a matsayin tada zaune tsaye daga wasu batagari.

Sanarwar ta ce, “Barka da warhaka kowa da kowa. An cika ni da kiraye-kirayen da sakonni da dama tsakanin jiya da yau kan wani mafi ma shugabancin EFCC. Ina so kawai in yi amfani da wannan damar don karyata wannan labarin kuma in ce ba gaskiya ba ne.

"Dole ne wannan bayanin ya fito ne daga masu yin barna kuma ya kamata a yi watsi da shi gaba daya." 

Daily Nigerian Hausa 

Post a Comment

Previous Post Next Post