Gwamnan Abba Kabir Yusuf Ya Mayar Da Barista Muhuyi Magaji Kan Muƙaminsa Na Shugabancin Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Na Jihar Kano.


Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin Shugaban Hukumar Sauraron Korafe-korafen Al'umma da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar Kano (PCACC), domin kammala wa’adinsa.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa, babban sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar ta Kano.

Idan za'a iya tunanwa, gwamnatin da ta gabata ta Abdullahi Umar Gnaduje ta dakatar da Muhuyi tare da tsige shi daga mukaminsa bayan majalisar dokokin jihar ta ce tana da shakku kan yadda yake gudanar da ayyukansa.

Sanarwar ta bayyana cewa Barista Muhuyi zai koma kan aikinsa ne nan take.

Rahoton BBC Hausa

Post a Comment

Previous Post Next Post