Zamfara Na Cikin Tasku A Cikin Bashi Nake Tafiyar Da Mulkina, In Ji Gwamna Dauda Lawan


 Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya ce tun da aka rantsar da shi har zuwa wannan lokaci a cikin bashi yake mulki, saboda gadar mulki ba tare da kudi ba a asusun gwamnati.


Gwamnan Lawan a wata tattaunawa ta musamman, ya yi bayani a kan yadda ya tarar da gwamnati bayan ya sha rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayu har zuwa wannan lokaci.


Ya ce babu wani abin da gwamnatinsa ta tarar a cikin lalitar Zamfara, sai naira miliyan uku kacal.


"Kusan asusu guda na gani, watakila ince akwai kamar naira miliyan uku ko hudu ne a ciki", in ji  Dauda.


Rahoton BBC Hausa. 

Post a Comment

Previous Post Next Post