"KUJI TSORON ALLAH, BA'A BAKU MUƘAMAI DON KU AZURTA KANKU BA"-GWAMNA BALA GA KWAMINISHINONINSA



Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed yayi kira ga sabbin kwamishinoninsa da aka rantsar da su rage tsadan gudanar da gwamnati sannan su ji tsoron Allah wajen sauƙe nauyin da ya rataya a wuyansu, ya kuma gargaɗe su kan cewa ba'a basu muƙamai don su azurta kan su ba. 

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin rantsar da sabbin kwamishinoni na jihar, inda yayi kira gare su da suna ziyartan al'ummominsu akai-akai domin samar da yarda cikin lamuran gwamnati. 

Yayinda yake taya su murna, gwamna Bala ya tunatar da su cewa an zaɓo su ne a matsayin wakilan mazaɓunsu, sannan anyi dubi ne ga cancanta, ƙwazo, ayyuka, gaskiya da jajircewa yayin zaƙulo su. 

Gwamnan Bala ya kuma bayyana ƙwarin gwiwansa kan sabbin kwamishinonin, inda yace daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2023, gwamnatin PDP ƙarƙashin jagorancinsa ta cimma nasarori da dama wajen samar da ababen more rayuwa da ayyukan raya al'umma wanda hakan yayi tasiri wajen samar da walwala ga al'ummar jihar. 

Daga ƙarshe gwamnan ya gargaɗi sabbin kwamishinonin kan cewa babu wani muƙami da ya fi wani, sannan su kiyaye anfani da muƙamansu wajen cimma nasu buƙatun son zuciya. 

Sabbin kwamishinonin da aka rantsar sune:

1. Maiwada Bello- Natural Resources 

2. Ibrahim Gambo - Works and Transportation 

3. Mahmoud Babamaji - Commerce and Industry 

4. Danlami Ahmed Kawule - Housing and Environment 

5. Dr Lydia Haruna Tsammani- Higher Education 

6. Ahmed Sarki Jalam - Local Government & Chieftancy Affairs 

7. Yakubu Ibrahim Hamza- Religious and Social Orientation 

8. Usman Danturaki- Information and Communication 

8. Abdu Hassan- Culture and Tourism 

10. Muhammad Salees -Youths and Sports 

11. Dr Yakubu Adamu -Finance and Economic Development 

12. Modibbo Abdulkadir Ahmed -Power, Science and Technology 

13. Hajara Yakubu Wanka- Humanitarian Affairs &Disaster Management 

14. Hajara Jibrin Gidado- Women Affairs &Child Developments 

15. Farouq Mustapha - Rural Development& Special Duties 

16. Aminu Hammayo -Budget ,Economic Planning & Multilateral Coordination 

17. Hassan El-Yakub SAN-Justice 

18. Mohammed Hamisu Shira - Cooperative & SMEs

19. Professor Simon M. Yalams- Agriculture 

20. Abubakar Abdulhamid Bununu Esq -Security &Internal Affairs 

21. Dr Jamila Mohammed Dahiru - Education 

22. Dr Adamu Umar Sambo - Health 

23. Abdurrazak Nuhu Zaki -Water Resources 

24. Amina Muhammad Katagum -Lands &Survey 

 ✍️ Abba Ibrahim 

Post a Comment

Previous Post Next Post