Zancen Gaskiya Game Da Buɗe Iyakokin Najeriya

Shugaban ƙasar Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin a buɗe iayakar Seme dake garin Legas domin a dinga shigo da motocin hawa kaɗai banda abinci. 

Darektan tafiye-tafiye ta titi a ma’aikatar sufurin Tarayya, Ibrahim Musa ne ya bayyana cewa za'a dawo shigo da motoci da duk abubuwan hawa ta iyakar kaɗai. 

Ibrahim Musa ya yi jawabin ne a wajen taron da kuniyar ECOWAS ta shiryawa jami’an Najeriya da Benin a jiya Laraba sakamakon koke-koke da ƴan kasuwa su ke yi. 

Don haka duk masu yaɗa cewa an bude sauran iyakokin Arewa ƙarya ne, iya iyakar Seme ta Legas aka buɗe domin ana shigo da motocin hawa banda abinci.

Daga Comr Abba Ibrahim Pantami  

Post a Comment

Previous Post Next Post