Labarin ƙarin albashi ba gaskiya ba ne - Fadar shugaban ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta ƙaryata rahoton da ya fito cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da karin albashi na yan siyasa da ma'aikatan shari'a.

Mai baiwa shugaban shawara kan ayyuka na musamman, Dele Alake ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis.

Ya ce karya ake yi cewa hukumar kula da albashi ta ƙasa RMAFC ta amince da ƙarin kashi 114 na albasahin shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa yan siyasa da kuma ma'aikatan bangaren shari'a.

Alake ya ce duk da cewa doka ta baiwa RMAFC dama ta yi ƙarin albashi, wannan labari dai na kanzon kurege ne. 

Daily Nigerian Hausa 

Post a Comment

Previous Post Next Post