Shalkwatar Tsaron Najeriya Ta Bai Wa Wasu Manyan Sojoji Zuwa Litinin Su Yi Ritaya


Shalkwatar tsaron Najeriya ta umarci manyan sojoji da suka haura kwas na 39 a makarantar horas da manyan sojoji da su ajiye aiki bisa raɗin kansu.

Matakin na zuwa ne bayan da Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabbin hafsoshin tsaron ƙasar.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar mai ɗauke da sa hannun Manjo janar Y. Yahaya a madadin babban hafsan tsaron ƙasar.

“An umarce ni na buƙaci duka manyan sojoji da ke sama da kwas na 39 na makarantar horas da manyan hafsoshin sojin ƙasar, su gaggauta miƙa takardun ajiye aiki bisa raɗin kai'', in ji sanarwar.

“Haka kuma ana buƙatar waɗanda umarnin ya shafa su mika takardun nasu ga shalkwatocin tsaron da suke aiki zuwa ranar Litinin 3 ga watan Yulin 2023''.

Bisa ga al'adar aikin soji, manyan jami'ai ba za su karɓi umarni daga sojojin da suka girma a aiki ba.

Dan haka naɗin sabbin manyan hafsoshin tsaron da shugaban ƙasar ya yi, zai tilasta wa manyan sojoji kusan 100 ajiye aikinsu.

Waɗanda suka haɗar da Janar-janar, da masu muƙamin Burgediya janar da masu muƙamin Air Vice Marshal da muƙamin Admirals a rundunonin sojin ruwa da na sama.

Shi dai sabon babban hafsan tsaron ƙasar Manjo Janar Christopher Musa ɗan kwas na 38 ne na makarantar horar da manyan hafsoshin tsaro, yayin da sauran manyan hafsoshin sojin ƙasa na sama da na ruwa su kuma 'yan kwas na 39 ne. 

Rahoton BBC Hausa 

Post a Comment

Previous Post Next Post