CIKA ALƘAWARI: Cikin Kwana 100 Zamu Rushe Duk Ginin Da Aka Yi A Filayen Da Basu Dace Ba, Kwanaki Ɗarin Farko Zasu Kasance Kwanakin Rusau Ne A Jihar Kano.

Mai Magana da yawun Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2019, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook cikin watan Maris na shekarar 2021 cewar idan Allah ya basu nasara a zaɓen Gwamnan Kano a shekarar 2023, a cikin kwana ɗarin farko zasu rushe duk wani gini da aka yi a filayen da basu kamata ba.

Bature ya ƙara da cewar, zasu cire dukkan sabbin Sarakunan da aka ƙirƙiro a Kano, tare da dawo da Khalifa Muhammadu Sunusi II kan karagarsa a matsayin Sarkin Kano guda daya tilo.

Ya cigaba da cewar, kwana darin farko zasu kasance kwanakin Rusau ne a jihar Kano, inda zasu bi duk wani fili ko gini da aka yi a inda bai dace ba su rushe shi.

Yanzu dai haka gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ɗauki miƙatin cika wannan alƙawarin. Ya kuke ganin illa ko tasirin cika wannan alƙawarin? 

Daga Abba Ibrahim  

Post a Comment

Previous Post Next Post